Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale

Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullah a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara

Hassan Fadlallah wanda dan majalisar kasar Lebanon ne daga kungiyar Hizbullah a bayyana cewa; gwargwadon yadda ake ja da baya a gaban makiya, suke kara samun karfin gwiwa,don haka da akwai bukatar hadin kai a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi domin fuskantar kalubalen dake gaba.

 Shi dai Hassan Fadlalalah yana halartar taron majalisun kasashen  nahiyar Asiya da ake yi a birnin Mashhad na Iran, ya bayyana cewa: Laifukan da ‘yan sahayoniya suke yi, yana nuni ne da yadda su ka kai koli wajen nuna keta a kan kasashen da suke da cin gashin kai da ‘yanci, da hakan yake a matsayin karya zaman lafiya da sulhu na duniya.

Fadlallah ya kuma yi jinjina ga jamhuriyar musulunci ta Iran akan tsayin dakarta a lokacin wuce gona da irin Haramtacciyar Kasar Isra’ila da kuma kare kanta da ta yi wanda halartacce ne kamar yadda dokokin kasa da kasa su ka yi tanadi.

Haka nan kuma ya ci gaba da cewa; Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kuma kai wasu hare-haren wuce akan kasashen Yemen da Qatar,wanda abin yin Allawadai da shi ne.

Dan majalisar kasar ta Lebanon ya kuma yi Ishara da yadda sojojin mamayar Haramtaccitar kasar Isra’ila suke kai wa kasar Syria hare-hare daga lokaci zuwa lokaci domin damfara ikonta a kan wannan kasa.

Bugu da kari, Hassan Fadlallah ya yi kira da dukkanin al’ummun larabawa da na musulmi da su  yi watsi da sabanin dake tsakaninsu domin fuskantar kalubalen da yake a gabansu.

A gefe daya, dan majalisar na Iran ya gana da shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Qalibaf, tare da mi ka masa gaisuwa daga shugaban majalisar dokokin kasar Lebanon Nabih Barry.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted