Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar

Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu

Kungiyar Hamas wacce take iko ga Gaza ta yi gargadin kan cewa, hare-haren da HKI take kaiwa a kan dukkan fadin Gaza a halin yanzu suna iya kawo karshen yarjeniyar zaman lafiya da ta cimma da ita.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa, kungiyar Hamas ta aiwatar da dukkan sharuddan tsagaita wuta wadanda aka dora mata, amma bangaren HKI ya ci gaba da keta tsagaita wutar tare da hare-haren da take kaiwa kan yankuna daban-daban na zirin Gaza, hare-haren da suka kai daruruwan Falasdinawa ga shahada ya zuwa yanzu.

Qassem ya ce tuni kungiyar ta shaidawa jami’an gwamnatin kasar Masar kan abinda HKI take yi na keta hurumin yarjeniyar tsagaita budewa juna wutan wanda bai kai watanni biyu ba.

Kasashen Masar, Turkiya da Qatar da Jordan da wasu kasashen larabawa da Musulmi ne suka dauki nauyin ganin an aiwatar da shirin tsagaita wutar kamar yadda ya dace.

Amma tun bayan tsagaita wuta yahudawan basu daina kashe Falasdinawa ba. Banda haka sun ci gaba da takaita kayakin abincin da ke shigowa Gaza sabanin abinda aka cimma da ita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted