Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar babban kwamandanmayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila.
Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.”
Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin na ‘yan sahayoniya.”
A gefe daya, ma’aikatar harkokin cikin gidan Iran ta yi tir da wannan laifin na ta’addanci da ‘yan sahayoniya su ka tafka ta hanyar kai hari akan rukunin gidajen fararen hula a cikin Beirut wanda ya yi sanadiyyar shahadar babban kwamanda na gwagwarmata Haisam Tabtaba’i.
Bayanin na ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ya kuma ce: “Abinda makiya su ka yi, keta tsagaita wutar yaki ne da aka cimmawa a cikin watan Nuwamba na 2024, kuma hari ne na dabbanci akan kasar da take da shugabanci da hurumi.”
Haka nan kuma ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta yi kira da a hukunta jagororin wannan tsarin na ‘yan sahayoniya da suke aikata laifukan yaki.