Rahotanni sun bayyana cewa daliban jami’ar St Gorges dake London sun yi zanga-zangar nuna adawa da daukar wani farfesa a fanni tattalin arziki kuma tsohon sojan Amurka aiki a makarantar, inda suka nuna kasancewarsa babban barazana ne ga dalibai musamman ga falsdinawa da kuma masu nuna goyon bayansu.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa daukar tsohon sojan isra’ila aiki yana Isar da wani mummunan sako ne ga dalibai kai tsaye musamman wadanda suka shafi rikicin dake faruwa a yankin gaza, kuma matakin da jamiar ta dauka yayi karo da alkawuran da ta dauka na bada ilimi da kuma kare hakkin dan adam.
Akalla dalibai magoya bayan falasdinawa fiye da 100 ne da magoya bayansu suka yi gangami a wajen jami’ar da kungiyar city action for palasdin ta dauka, inda suka bukaci a kori ben-Gad cikin gaggawa saboda aiki da yayi a matsayin sojan Amurka a shekara ta 1982 zuwa 1985.
Shi dai Ben-gad yayi aiki a matsayin sojan Amurka a shekara ta 1982 alokacin kisan kare dangin Sabra da shatila da isra’ila ta yi kan dubban falasdinawa da yan labanon.