Nigeria:Kotu Ta Yanke Wa Nnamdi Kanu Hukuncin Zaman Kurkuku Na Har Abada  

A zaman da kotun ta yi a birnin Abuja a yau Alhamis, mai shari’a James Omotosho ya yanke hukuncin cewa mai shigar da kara ya

A zaman da kotun ta yi a birnin Abuja a yau Alhamis, mai shari’a  James Omotosho ya yanke hukuncin cewa mai shigar da kara ya gabatar da kwararan dalilai akan yadda jawaban da Kanu ya rika watsawa su ka ingiza mambobin haramtacciyar kungiyar ” IPOB” su ka kai wa jami’an tsaro hari a yankin kudu maso gabashin kasar.

Mai shari’ar ya bayyana Kanu a matsayin wanda ya shirya ayyukan  da su ka kai ga yin ta’addanci.

A 2009 ne dai Kanu ya fara watsa shirye-shiryen Rediyo Bi’afara daga London, da yake Magana da ‘yan kungiyarsa ta IPOB.

Tun da fari dai Alkalin ya bayar da umarnin a fitar da Nnamdi Kanu daga cikin kotun sabdoa abinda ya kira rashin da’a daga gare shi.

Alkalin kotun koli ta tarayyar Najeriya dake Abuja, ya bayar da umarnin a fitar da shugaban kungiyar ‘yan awaren Biafra ( IPOB) daga cikin kotu saboda rashin da’ar da ya nuna gababin yanke hukunci a yau Alhamis.

Mai shari’a James Omotosho ya yi watsi da wasu kararraki sabbi da Kanu ya shigar saboda rashin dacewarsu.

Shi dai Kanu yana fuskantar shari’a ne akan tuhumar ayyukan ta’addanci da kungiyarsa ta “IPOB” mai son kafa kasar Biafara ta ‘yan kabilar Igbo.

Mai shari’ar ya kuma ce; saboda rashin da’ar Kanu da kuma halayyarsa ta son rikici, za a yanke hukunci ne ba tare da halarci zaman kotun ba.

 A lokacin da mai shari’a yake kokarin yanke hukuni ne dai Kanu ya furta cewa ba shi da hakkin yin hakan saboda bai rubuta jawabinsa na karshe ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted