Ribadu Ya Jagoranci Tawagar Nijeriya Zuwa Amurka Kan Zargin Yi Wa Kiristoci Kisan Gilla

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci.

Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza.

A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin.

Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci.

A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi magana a kan zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya.

Tawagar Nijeriya, wacce ta haɗa da manyan jami’ai kamar Bianca Ojukwu, Kayode Egbetokun, da Lateef Fagbemi, sun gana da Moore don bayyana ƙalubalen tsaro, yaƙi da ta’addanci, da kare al’ummar ƙasar.

Moore, ya ce tattaunawar “ta kasance ta gaskiya, kuma mai amfani” kuma ya jaddada cewa Amurka na son ganin an dauki matakai don kare Kiristoci daga tashin hankali da ta’addanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted