Kasashen Iran Da Malesiya Sun Rattaba Hannu Kan Jarjejeniyar Fadada Dangantakar Addini

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar,

Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi  adaidai lokacin da kasashen musulmi suke fuskantar matsalolin aladu da tasirin kasashen yamma a tsarin zaman takewarsu da tashe tashen hankula na siyasa musamman ma kan yankin falasdinu.

Kasashen biyu suna da matsaya daya na dogon lokaci a bangaren abincin Halal, aladun musulunci da kuma ilimin Addinin, don haka wannan tattaunawar da aka yi an sake sabunta alakar ne bisa ababen girmama wa na musulunci da kare iyali da kuma bunkasa karatun alkur’ani tare da yin aiki tare.

Zulkaranen bin Hassan mataimakin ministan harkokin Addini na kasar malesiya ya jinjinawa matsayin iran akan gwamnatin sahyuniya da kuma goyon bayan da take bawa alummar falasdinu da ake zalunta ya bayyanata a matsayin cibiyar hadin kan musulmi .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted