Turkiyye na karbar taron Kasashen Musulmi Kan Halin Da Ake Ciki A Gaza

Turkiyye na karbar bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan halin da ake ciki a Gaza. Wannan taron ya zo ne bayan makonni

Turkiyye na karbar bakuncin wani taron ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan halin da ake ciki a Gaza.

Wannan taron ya zo ne bayan makonni uku da fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

A cewar Turkiyya, manufar taron ita ce taimakawa wajen mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sake tabbatar da rawar da take takawa a wannan batu.

Ƙasashen musulmin dake halartar taron na yau Litini a Istanbul su ne wadanda Donald Trump ya aminta dasu don tabbatar da nasarar shirin zaman lafiya na Gaza.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyye Hakan Fidan, wanda ke karbar bakuncin takwarorinsa, ya gabatar da wannan taron a matsayin hanyar yin nazari kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta, samar da matakai na gaba, da kuma daidaita su kafin tattaunawa da kasashen Yamma.

Haka kuma hanya ce ga wadannan kasashen da suka fi yawan al’ummar Musulmi su nuna jajircewarsu wajen kiyaye yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya bayyana tsagaita wuta a matsayin mafi rauni idan aka yi la’akari da kalubalen da mataki na biyu na shirin ke fuskanta.

Mataki na biyu na shirin na Trump ya tanadi kwance damarar makamai na kungiyar Hamas, samar da rundunar sulhu, da sauransu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted