Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari

Naurorin tauraron dan adam sun nuna hoton yadda sojojin Amurka suke kara kusantar kasar venuzuwela ciki har da jiragen yaki masu kai hare-hare duk da

Naurorin tauraron dan adam sun nuna hoton yadda sojojin Amurka suke kara kusantar kasar venuzuwela ciki har da jiragen yaki masu kai hare-hare duk da yake cewa shugaban Amurka Dolad trump ya karyata batun da ake yi na yunkurin kai mata harin soji,

Wannan matakin yana daya daga cikin yadda sojojin ruwan Amurka suka mayar da hankali a yankin karebiya, wanda hakan ya haifar da damuwa a latin Amurka game da yiyuwar daukar matakin soji na bangare daya kan kasar Venuzuwela ba tare da izinin majalisar dinkin duniya ko kuma kasashen duniya ba,

Washington ta yi ikirarin cewa za ta kai hari kan masu fataucin miyagun kwayoyi ne sai dai masu sa ido kan alamuran yankin sun bayyana cewa yanayin yadda ake turawa da sojoji da makamai a yankin  yana nuna shirin da ake yi ne na daukar matakin soji ko kuma matsin lamba kan gwamnati venuzuwela don ta mika wuya.

Ana sa bangaren shugaban kasar venuzuwela yayi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ya dauki mataki kan harin da Amurka ta kai kan wasu jirage dake kusa da ita a matsayin haramtacce kuma ta kare yancin kasar venuzuela

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted