Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini

Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini. Shugaban

Shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya fada wa Shugaban Amurka Donald Trump cewa; a Nigeria ba a lamunta da duk wani rikicin addini.

Shugaban na kasar Najeriya ta mayar wa da Donald Trump martani ne saboda yadda ya bayyana Najeriya a matsayin “kasa mai damuwa ta musamman”, bisa zargin cewa Mabiya addinin kiristanci suna fuskantar barazanar karewa, ya kuma yi alkawalin cewa Amurkan za ta ba su kariya.

Donald Trump ya ce; Kiristoci suna fuskantar barazanar karar da su a Nigeria, an kuma kashe dubban kiristoci a kasar.”

A yau Asabar, kwana daya daga wancan zancen na Trump ne dai shugaban kasar ta Nigeria Bola Ahamd Tinubu mayar da martanin da ya kunshi cewa:  Nageria kasa ce ta Demokradiyya, kuma tsarin mulkinta ya lamuncewa kowa ‘yancin yin addini.”

Har ila yau shugaban kasar ta Najeriya ya ce; Tun daga 2023 gwamnatinmu take mu’amala da hulda da dukkanin malaman kirista da musulmi, kuma tana ci gaba da magance matsalar tsaro da ta shafi dukkanin mutanen kasar daga kowane addini a cikin yankunan kasar.

Shugaba Tinubu ya kuma ce; Bayyana Nigeria a matsayin kasa wacce ake fada da addini, ba ya nuni da hakikanin yadda rayuwa take a kasar, kuma ba a yi la’akari da yadda gwamnati take aiki tukuru domin kare ‘yancin yin addini da akidun mutanen Nigeria ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted