Mayakan Kungiyar Kurdawa Ta PKK Sun Fice Daga Turkiyya Zuwa Iraki

Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar

Kungiyar Kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga Türkiyya zuwa arewacin Iraki

Kungiyar kurdawa ‘yan tawaye ta PKK ta sanar da janye dukkan dakarunta daga cikin kasar Turkiyya zuwa arewacin Iraki a yau Lahadi.

Kafafen yada labarai sun ambato wata sanarwa daga kungiyar ‘yan tawayen kurdawar tana cewa: “Ta janye dukkan mayakanta daga cikin kasar Turkiyya zuwa yankunan arewacin kasar Iraki.

A watan Fabrairun da ya gabata ne, Abdullah Ojalan, wanda ya kafa kungiyar Ma’aikata ta Kurdistan (PKK) a Turkiyya, ya yi kira da a rusa kungiyar, yana mai kira ga mayakan kungiyar da su ajiye makamansu su koma ga daukar matakin siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted