Wani Masani Dan kasar Iran Ya Samu Lambar Yabo Ta WHO A Yankin

Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin

Dr Majid Ghayour Mubarhan kwararre kuma farfesa a jami’ar kiwon lafiya ta birnin mashahada ya samu kyautar hukumar WHO na gabashin meditareniya saboda namijin kokarin da yayi na kirkiro abin da zai kula da kuma kare kamuwa da cututtuka da basa yaduwa, kamar cutar kansa ciwon zuciya da kuma ciwon Sugar.

Wannan kyautar tana nuna irin ci gaban da Iran ta samu ne a bangaren kimiyyaa yankin duk da takunkumi da kuma takurawar da take fuskanta daga bangaren kasashen turai dake takaita halartar masana kimiyyar kasar  hallara a matakin kasa da kasa.

A duk shekata hukumar lafiya ta duniya tana bada kyauta ga duk wani masanin kimiya da yayi kwazo wajen kirkiro wata fasaha a bangaren lafiyar gama gari,  da kare kamuwa daga cututtuka, kyautar wannan shekarar wata cibiyar bada kyaututtuka ne dake kasar Kuwaiti ta samar, kuma aka bawa Dr Ghayour mobarhan saboda gudunmawar da ya bayar wajen kare kamuwa da cutar zuciya,

Sai dai saboda rashin samun visa a akan lokaci bai samu halartar wajen taron ba, amma Dr Riza’i mataimakin ministan lafiya na Iran ya karbi kyautar a Madadinsa,

Dr Ghayour shi ne wanda ya kafa cibiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ta Unesco a iran babbar cibiyar hadin guiwa ta bincike a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted