Sudan: Jirgin ‘Drone’ Ya Fada Kan Tashar Jiragen Sama Na Khurtum Kafin A Sake Bude Ta

Labaran da suke fitowa daga birnin Khartum babban birnin kasar Sudan sun bayyana cewa jirgin yaki na kunan bakin wake ya fada kan wani yanki

Labaran da suke fitowa daga birnin Khartum babban birnin kasar Sudan sun bayyana cewa jirgin yaki na kunan bakin wake ya fada kan wani yanki kusa da tashar jiragen sama na birnin kwana guda kafin gwamnatin kasar ta sake bude ta fiye da shekaru biyu da sufe ta.

Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa an rufe tashar jiragen sama na Khurtum ne, jim kadan bayan fara yaki da a cikin watan Afrilun shekara ta 2023.  Yaki tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun  ‘ Rapid Support Forces (RSF), dakarun daukin gaggawa wanda ya lalata muhimman kayakin aiki a tashar, hakan ya sa aka rufe ta.  

Wakilin kanfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana wadanda suka ganewa idanunsu sun fada masa cewa sun ji karar jirgin yakin a tsakiya da kumakudancin birnin Khartum da misalign karfe 4-6 na safem sannan bayan haka suka ji karar tashin boma bomai a kusa da tashar.

A ranar litinin da ta gabata ce hukumomin tashar jiragen saman suka bada sanarwan cewa a yau Laraba ne za’a sake bude tashar jiragen saman da jiragen cikin gida.

Zaman lafiya ta dawo a birnin Khartum babban birnin kasar ta Sudan bayanda sojojin kasar sun dawo da ikon gwamnatin kasar a kansa. Sai dai har yanzun ana fama da hare-haren Drones na RSF daga lokaci zuwa lokaci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted