Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza

Kasashen Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza Ministan harkokin wajen Iran

Kasashen Iran da Iraki sun bukaci duniya da ta dakatar da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Gaza

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da mai baiwa kasar Iraki shawara kan harkokin tsaro Qasim al-Araji sun bukaci kasashen duniya da su dakatar da kisan gillar da gwamnatin Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a zirin Gaza.

Al-Araji, wanda ke jagorantar wata tawagar jami’an tsaro a kasar Iran, ya gana da Araghchi a yammacin jiya Litinin, inda suka yi musayar ra’ayi da su kan hanyoyin inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma tattauna halin da ake ciki a Gaza da Lebanon.

Dukkan jami’an biyu sun bayyana damuwarsu kan yadda Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, sannan sun bukaci kasashen duniya da su dauki matakin dakatar da kisan kiyashi da laifukan da gwamnatin mamaya ke yi wa Falasdinawa, tare da tabbatar da isar da kayan agajin jin kai.

Araghchi ya bayyana kyakkyawar alakar da ke tsakanin Tehran da Bagadaza daga dukkan fannoni, inda ya jaddada bukatar ci gaba da tuntubar juna da karfafa hadin gwiwa kan harkokin tsaro, musamman a fannin kula da kan iyaka.

Al-Araji ya kuma yi wa Araghchi bayanin ci gaban da aka samu wajen aiwatar da yarjejeniyar tsaro ta tsakanin Iran da Iraki, yana mai jaddada aniyar Bagadaza na ci gaba da tabbatar da ita.

Ya yaba da hadin kai da tsayin daka da al’ummar Iran suke da shi wajen tunkarar wuce gona da iri na kasashen waje, yana mai tabbatar da cewa Iraki ba za ta taba bari a yi amfani da yankinta wajen yin barazana ga ‘yancin kai ko tsaron kasar Iran ba. Bangarorin biyu sun kara jaddada bukatar hadin kan kasashen musulmi wajen tunkarar manufofin wuce gona da iri na Isra’ila

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted