Iran: IRGC Sun Bayyan Shirinsu Na Karfafa Dabarun Hadin Guiwa Da yamen

Dakarun kare juyin musulunc na kasar iran ta bayyana cewa tana da cikakken shiri na kafa fadada dabarun yin hadin guiwa da dakarun karejuyin musulunci

Dakarun kare juyin musulunc na kasar iran ta bayyana cewa tana da cikakken shiri na kafa fadada dabarun yin hadin guiwa da dakarun karejuyin musulunci na kasar yamen wajen kalubalnatar kasashe ma’abota girman ai da kuma yan sahyuniya.

A cikin sakon da kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran ya fitar a jiya lahadi mojor ganar mohammad pakpur ya aike da sakon ta’aziya ga babban hafsan hafsoshin sojin kasar Yamen  brigadier janar Yousef hassan al’madani na shahadar major ganar mohammad abdular karin al’gamari wanda yayi fama da rashin lafiya sakamakon rauni da ya ji a harin da isra’ila ta kai masa a watan Augusta  tare da wasu abokan aiki  har da dan sa mai shakara 13.

Har ila yau ya taya madani murnar rantsar da shi da aka yi a matsayin sabon hafsan hafsoshin sojin kasar, kana ya yi masa fatar samun nasara da kuma ci gaba da bin hanyar da algamari ya bari, da kuma kara kaimi da tsayin daka kan makiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted