Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta

Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar

Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017.

Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021.

Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995.

Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki.

Haka nan kuma shugaba Tinibu ya yafewa Sir Herbert Macaly dan kishin kasa da ya yi fada da ‘yan mulkin mallaka. ‘Yan mulkin mallaka ne su ka yanke masa hukunci a 1913.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted