Kungiyoyin matasa na ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Morocco, Sarkin Mohammed na shida, ya bukaci zababbun jami’ai a kasar da su daina jan kafa wajen kyautata rayuwar al’ummar kasar, yana mai cewa inganta harkonin ilimi da kiwon lafiya shi ne abinda ya kamata a fi ba muhimmanci.
An jima ana dakon jawabin sarkin na wannan juma’a, tun bayan da masu zanga-zangar, suka fara mamaye titunan biranen kasar kusan ko wanne dare tun daga ranar 27 ga watan da ya gabata na Satumba.
Masu zanga-zangar dai wadda ake yiwa lakabi da Gen Z, na ci gaba da kiraye-kirayen kawo sauyi, ko da yake a yayin jawabin Sarkin na wannan Juma’a bai yi magana kai tsaye game da ita ba.
Wannan zanga-zanga dai, ta samo asali ne bayan samun rahoton mutuwar wasu mata masu juna su 8 a asibitin gwamnati na birnin Agadir, kuma ita ce mafi girma cikin shekaru da matasan Kasar suka yi domin nuna kin jinin gwamnati, inda suka bukaci a inganta fannin lafiya da ilimi, tare kuma da suka kan kashe biliyoyin kudi domin gyara filayen wasan kwallon ƙafa da za a buga wasan cin kofin duniya.