Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya

Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela

Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya

Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a.

Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin tekun Caribbean. Na biyu, daukar matakan da suka dace don hana ci gaba da tabarbarewar al’amura. Na uku, a amince da wani kuduri da ya wajabta wa dukkan mambobin su mutunta ‘yancin kai da daukan Venezuela a  matsayar kasa mai cin gashin kai”.

Jami’in diflomasiyyar na Venezuela ya zargi Amurka da aiwatar da kashe-kashen gilla, yana mai cewa “gwamnatin Amurka ta amince da kai hare-haren bama-bamai kan kananan jiragen ruwa guda hudu a tekun Caribbean, inda suka kashe fararen hula 21 da ba su dauke da makamai.” Ya bayyana wadannan ayyuka a matsayin “kisa ba bisa ka’ida ba” ba na kare kai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted