Burtaniya: An Ci Gaba Da Zanga-Zangar Goyon Bayan Falasdinawa Duk Tare Da Gargadin Jami’an Tsaro

Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir

Dalibai da malaman Jami’o’i a kasar Burtania sun bar ajujuwansu don halattar ganganmi a cikin jami’o’insu, na goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin tir da gwamnatin kasar saboda goyon bayan da take bawa HKI a kissan kiyashi, wanda ya kai shekaru biyu kenan a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa  zanga zangar bata takaita a jami’o’in birnin London kadai ba, sai dai an gudanar da su a manya –manyan biranen kasar duk tare da gargadin jami’an yansandar kasar kan cewa an haramta zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a kasar.

Sauran biranen da aka gudanar da gangamin dai sun hada Glasgow, Manchester, Bristol, Sheffield da Edinburgh.

Daliban da kuma malamansu suna rera taken “Yanci ga Falasdinu daga teku har kogi” “HKI yar ta’adda ce’ ‘A daina sayarwa HKI makamai’ da sauransu.

Ya zuwa shekaru biyu da suka gabata dai HKI ta kashe Falasdinawa kimani dubu 67,000 a gaza a yayinda wasu kimani 180,000 sun ji rauni, sai kuma wasu kimani 10,000 sun bace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted