Gidauniyar Mandela ta yi tir da Isra’ila kan dakile ayyukan jin kai zuwa Gaza

Gidauniyar Nelson Mandela ta yi Allah wadai da Isra’ila kan dalike duk wani yunkuri na ‘yan fafatuka dake kokorain shigar da kayan agajin jin kai

Gidauniyar Nelson Mandela ta yi Allah wadai da Isra’ila kan dalike duk wani yunkuri na ‘yan fafatuka dake kokorain shigar da kayan agajin jin kai zuwa Gaza.  

Gidauniyar ta ce ba zai yuwu a yi shiru ba dangane da dakile ayyukan jin kai a Gaza da kuma tsare wadanda ta kira “masu kare mutuncin bil’adama.”

A cikin wata sanarwa da Gidauniyar ta fitar, ta yi kakkausar suka kan katsalandan da Isra’ila ta yi wa jirgin ruwa na Sumud Global Flotilla dake shirin shiga Gaza domin aikin jin kai.

Daga bisani gidauniyar wacce kungiya ce mai zaman kanta ta Afirka ta Kudu da aka kafa domin ci gaba da dawwamar da tafarkin shugaban kasar bakar fata na farko a Afirka ta Kudu ta bukaci a gaggauta sakin duk masu fafutuka da gwamnatin Isra’ila ke tsare da su ba bisa ka’ida ba.

Gidauniyarta kuma nuna matukar damuwa kan rahotannin kutse da sojojin Isra’ila suka yi wa jiragen ruwa dauke da masu fafutuka na kasashe daban-daban da kuma agajin jin kai zuwa Gaza.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted