Gaza: Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren Isra’ila ya kai 66,148

Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma

Adadin wadanda suka yi shahahda a yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke aiwatarwa kan al’ummar yankin zirin Gaza ya kai shahidai 66,148 da kuma jikkata wasu 168,716, tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Bisa kididdigar baya-bayan nan da ma’aikatar lafiya ta zirin Gaza ta fitar, adadin wadanda suka yi shahada tun bayan da sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka koma yakin kisan kare dangi a ranar 18 ga watan Maris ya kai 13,280, kuma adadin wadanda suka jikkata ya kai 56,675.

A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mutane 51 ne suka yi shahada wasu 180 kuma suka jikkata a zirin Gaza.

A halin da ake ciki dai, wani adadi mai yaw ana  wadanda abin ya shafa na ci gaba da zama a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, inda motar daukar marasa lafiya da ma’aikatan agaji suka kasa isa gare su, sakamakon tarin baraguzan gine-gine da kuma hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaddamarwa.

Bugu da kari, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kashe wasu Falasdinawa hudu tare da jikkata wasu 57 sakamakon harin da ‘yan ta’addan suka kai kan masu neman agaji, lamarin da ya kai adadin mutanen da suka yi shahada a fafutukar neman abinci zuwa 2,580 da kuma jikkatar wasu sama da 18,930.

A cikin wannan lokaci, ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta ba da rahoton shahadar  mutane biyu a sakamakon kamuwa da matsananciyar yunwa da Isra’il ta haifar a yankin, daga cikinsu  har da wani yaro. Wannan ya Sanya adadin wadanda yunwa ta kashe ya karu mutane  455, ciki har da yara 151.

Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya kuma tabbatar da cewa ikirarin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi game da ba da izinin zirga-zirgar ‘yanci zuwa kudu tsabar karya ce da kuma kokarin wawantar da duniya domin boye gaskiyar abin da yake faruwa na ayyukan yakin da take tafkawa a kan mazauna yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted