Larijani: Iran za ta katse hadin gwiwa da IAEA idan aka dawo mata da takunkuman MDD

Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta

Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da  takunkuman Majalisar Dinkin Duniya.

Sakataren Majalisar ta Iran Ali Larijani ya sake nanata kudurin Iran na cewa ba da ta niyyar yin amfani da makamin nukiliya – ko dai a yanzu ko a nan gaba.

Ya kuma ce ayyukan wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni ya sanya tattaunawar ta zama “bazara”.

Yau Juma’a ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama domin kada kuri’a kan kudurin da Rasha da China suka gabatar na dage batun sake kakaba takunkuman na MDD kan Iran.

Idan kwamitin ya gaza amincewa da kudurin, Majalisar Dinkin Duniya za ta kakabawa Iran takunkumi a gobe Asabar.

A cikin tattaunawar da akayi da shi, Larijani ya ce, “Mun bi duk wata hanya da hanyoyin da aka tanada domin magance wannan rikici cikin lumana.”

Ya kuma gargadi shugaba Donald Trump na Amurka cewa Iran ba za ta taba mika wuya ba idan har aka kai wasu sabbin hare-hare.

Dama kafin hakan Ministan harkokin wajen Iran Abbas Agarachi ya yi gargadin cewa Iran za ta yi watsi da yarjejeniyar da ta kulla ta barin jami’an MDD masu sanya ido kan nukiliya su duba cibiyoyinta, matukar kasashen Yamma suka sake kakaba mata takunkumi.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya na ta kokarin ganin ta gyara alakarta da Iran domin komawa kan aikin sanya ido kan shirin nukiliya na kasar, tun bayan harin da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliyarta a watan Yuli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted