Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa

Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa,

Wani makami mai linzami na Yemen ya tilastawa jirgin saman fira ministan gwamnatin Isra’ila saukar gaggawa

Kafofin yada labaran yahudawan swahayoniyya sun watsa rahoton cewa, an tilastawa jirgin saman Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu yin saukar gaggawa a lokacin da ake atisayen soja bayan harba makami mai linzami daga kasar Yemen zuwa yankunan Falasdinawa da aka mamaye.

Kafofin yada labarai sun ruwaito cewa, makamin da aka harba a yankunan da aka mamaye a shekarar 1948, jiya, Talata, ya tilastawa miliyoyin yahudawan sahayoniyya tserewa maboyan karkashin kasa.

An yi ta jin karar harbe-harbe ta sama a yankuna da dama na yankunan Falasdinawa da aka mamaye, tare da jin karar fashewar abubuwa masu karfin gaske.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted