Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Dauki Mataki Wajen Kawo Karshen Rashin Hankalin Isra’ila.

Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin

Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu.

A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel.

Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game  da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta.

Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar dakatar da bude wuta a Gaza sun tsira sai dai mutane 5 daga mambobin kungiyar tare da kuma da wani jami’in tsaron kasar Qatar ne suka mutu sakamakon harin na isra’ila ,

Kasar Amurka ta nisanta kanta daga kai harin, inda shugaban Amurka Donal trump ya bayyana cewa bashi da wani cikakkiyar masaniya kan harin na Isara’ila,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted