Aragchi: Yarjeniya Da IAEA Ya Nuna Hakurin Iran Bayan Hare-Hare Kan Cibiyoyin Nukliyarta

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa takaitacce hadin kai ta bawa hukumar IAEA a yarjeniyar da ta cimma da Gorris a birnin Alkahira. Ya nuna irin hakurin da JMI ta nuna bayan hare-haren da aka kai mata kan cibiyoyin Nukliyar kasar .

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar haka a yau a shafinsa na X kan cewa, Iran ta amince da takaitaccen aiki da hukumar IAEA ne saboda dole ne ya zamanto ana kula da ayyukan nukliyar kasar ko da takaitacce ne. Sannan ya ce kasar tana son ci gaba da raya yarjeniyar JCPOA na shekara ta 2015.

Ya ce, Iran ta amince da wannan takaitaccen yarjeniya ne bayan ta yanke hulda da hukumar IAEA kwata-kwata bayan hare-haren da Amurka da HKI suka kai kan cibiyoyin nukliyar kasar. Kuma duk wani sabon harin da zasu kaiwa kasar nan gaba zai bata wannan takaitaccen yarjeniyar.

Ya kuma gargadi kasashen yamma kan cewa, Iran zata tsaurar sharuddan da ta shimfiya a duk lokacinda aka sama masu ko aka kaiwa cibiyoyin Nukliyar  kasar hare-hare.

Sanna ya kammala da cewa, yarjeniyar NPT ba ta da bayani da ya shafi halin da Iran take ciki don haka a yarjeniyar wucun gadin da ta cimma da Grossi akwai wasu karin bayanai da aka kara wanda zai hada da halin da irin take ciki na amincin ayyukanta na Nukliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted