Kamfanin Kasar China Ta Sami Nasarar Samun Aikin Gina Titi Tsakanin Chadi Da Kamaru

Kasar China ta yi nasarar samun yardar hukumomin kasar Kamaru na gina titi na harkokin kasuwanci tsakanin kasar da Chadi har’ila yau da kasashen makobta

Kasar China ta yi nasarar samun yardar hukumomin kasar Kamaru na gina titi na harkokin kasuwanci tsakanin kasar da Chadi har’ila yau da kasashen makobta a kasashen tsakiyar Afirka zasu amfana da titin..

Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Labanon ta bayyana cewa, nesa da yadda kasashen Afirka suka saba na kulla irin wannan kontragi mai tsoka, a wannan karon kasashen Afirka suna samun karfin tsallaka wadan nan manya-manyan kasashen da suka saba danne su, zuwa ga abinda suka ga zai fi amfanarsu.

Wani kamfanin gine-gine na kasar China ya samu nasar samun kontragin gina wani babban titin wanda zai taso daga Duala na kasar Kamaru zuwa Njamena babban birnin kasar Chadi. Wanda masana suna ganin samun wannan titin zai kawo riba na kashi 35% na binda ake samarwa na harkokin kasuwa a kan wannan titin ga kasar Kamaru, sannan wasu kashi 35% na kayakin kasuwanci zai amfani mutanen yankin sannan wasu 20% ga mutanen kasar Chadi.

Ana saran kamfanin na kasar China zai kammala wannan aikin nan da shekara ta 2030. Ana saran idan wannan aikin ya kammala zai zama hanya kyautata tattalin arziki kasar Chadi, wacce take nesa da teku. Don zata hada kasar ta tekun Atlantika dake kudancin kasar kamaru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted