An Gudanar Da Zanga zangar Adawa Da Ziyarar Shugaban Amurka a Malaysia

Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gobe

Daruruwan kungiyoyin sa kai ne suka gudanar da zanga-zanga a kasar malesiya domin nuna adawa da ziyarar shugaban Amurka Donal Trump a karshen watan gobe saboda nuna goyon bayan isra’ila kan kisan kare dangi da take yi a Gaza, ,

 sun bukaci gwamnati da ta soke gayyatar wanda suka bayyana shi a matsayin babban mai laifin yaki dake da hannu wajen kisan kare dangi da isra’ila ke yi wa alummar Gaza, da hakan ya sabama dukkan dokokin kasa da kasa.

Mazu zanga zangar sun daga kwalaye da a ciki aka rubuta cewa trump kada ka zo,kuma mafiywancin wadanda suka halarci zanga-zangar mata ne da yara, kuma kungiyar dake nuna goyon bayan falasdinu ce ta jagoranci zanga-zangar,

fira ministan malesiya anwar Ibrahim ya amince da zuwan shugaban na Amurka bayan wasika da ya aike masa na halartar babban taron da zaa yi a yammacin Asiya, da gwamnatocin kasashen dake yanki , taron da ake son gudanarwa a makon karshe na watan oktoba mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted