Muhammad Baqir Qalibaf, Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada bukatar da ke akwai ga al’ummar Musulmi da su yi Allah wadai da kisan kiyashin da ake yi a Gaza ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma yi kira ga gwamnatocin kasashen musulmi da su yi koyi da al’ummarsu da suka dauki matakai na zahiri don nuna rashin amincewa da duk wata hanyar aiwatar da kashe-kashen yahudawan sahayoniyya.
A farkon taron majalisar a ranar Laraba, Qalibaf ya taya al’ummar musulmi murnar shigowar makon hadin kai, inda ya ce: A wadannan ranaku da ake gudanar da murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) suna tunawa da sakonsa na gina al’umma bisa imani da hankali da soyayya, tare da kira ga musulmi da su rungumi tausayi da hadin kai.