Iran ta shiga cikin tsirarun kasashe wadanda suke da fasahar kera motocin jigilar ma’adinai ADAK 150AC. Tare da tsarawa da kuma gina shi a cikin gida 100%.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI kasar shiga cikin tsirarun kasashen duniya wadanda suke da fasahar gina irin wadannan motoci wadanda ake amfani da su a wuraren aikin tono ma’adinai.
Labarin ya kara da cewa wannan ci gaban ba kawai ya nuna irin ci gaban fasahar kere-keren da kasar take da ba, sai dai kokari ne tabbar da cewa kasar ta wadatu daga saya ko kuma shigo da manya-manyan motoci da injuna daga kasashen waje, wadanda suke da tsada suke kuma da cikin kudi wadan kula da su.
Wannan yana daga cikin shirin kasar na ‘tattalin arziki mai juriya’ wanda Imam Sayyid Khamenei ya cusawa mutanen kasar, don basu damar tsayuwa da kansu da kuma jurewa dukkan matsin lamba daga kasashen waje.
Samarsa da wannan motar ADAK 150AC ya kawo karshen dogaro mai tsawo wanda kasar Iran take yi kan kasashen yamma a fagen hako ma’adinai da kuma sarrafa su. Wanda kuma ya fi saukin samarwa da kuma kula da shi. Wannan kuma ya shafi duk abinda Iran take bukata ko zata bukata don dogaro da kanta, ba tare da mika hannu ga wata kasar waje don cimma hakan ba.