Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yammacin Turai sun fara amfani da takunkumi kan kasar Iran bisa umarnin ‘yan sahayoniyya da Amurka
Dangane da matakin da kungiyar gungun Turai ta dauka na son sake dawo da takunkumin da ya shude kan kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Kasashe uku na Turai ne suka fara aiwatar da shirin sanya takunkumi bisa umarnin ‘yan sahayoniyya da Amurka. Baqa’ ya fara taron manema labarai na mako-mako da jajantawa al’ummar Yemen da Falastinawa, yana mai cewa: “A yayin da ake gudanar da juyayin shahadar fira ministan kasar Yemen da kuma wasu ministocin kasar a matsayin wani bangare na wuce gona da iri na sojojin ‘yan sahayoniyya, wannan matakin babban laifi ne kuma ya ci karo da dukkanin ka’idojin dokokin kasa da kasa, kuma wannan ta’addancin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar kisan kiyashi a Gaza.”
Baqa’i ya kara da cewa: “Suna ganin yadda ake kashe Falasdinawa a layin abinci da yunwa da kishirwa, adadin yana da matukar girgiza, inda aka kashe kimanin mutane 2,500 a layin abinci, abin bakin ciki shi ne, Majalisar Dinkin Duniya ba ta dauki wani kwararan matakai na dakatar da kisan kiyashi ba, ko kuma daura alhakin aikata laifukan yaki, saboda ci gaba da goyon bayan da Amurka ke ba wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yayin da kafafen yada labarai da ‘yan jarida ba su da kafar yada labaran duniya fiye da 50 da suka gudanar da ayyukansu na sa ido na kasa da kasa. shafukan farko a jiya, inda suke nuna kyamar al’ummar duniya kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza.”