Aragchi Yayi Tir da Kissan Firaiministan Kasar Yemen Da Wasu Ministocinsa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da kissan da sojojin HKI suka yiwa firay ministan kasar Yemen Ahmad Al-Rahawi da wasu

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya yi tir da kissan da sojojin HKI suka yiwa firay ministan kasar Yemen Ahmad Al-Rahawi da wasu jami’an gwamnatinsa. Ya kuma kara da cewa irin wadan nan hare-haren suna zagon kasa ga zaman lafiya a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a wani sakon da ya aika ga gwamnatin kasar Yemen da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin na marasa imini, wanda sojojin HKI suka yi. Ministan ya yaba da yadda kasar Yemen ta tsaya kan kafafuwanta wajen taimakawa mutanen Gaza wadanda ake zalunta. Aragchi ya ci gaba da aibata MDD kan rashin daukar mataki kan HKI a yayinda an kusan shekaru 2 da fara kissan kiyashi a gaza.

Ya kuma kammala da cewa wadan nan hare-haren tsoro ne tunda ba wata nasara da zata samu a irinsa, don ba zasu gabatar ko su maida wani abu baya ga kasar Yemen ba, a abinda tasa a gaba. Yayi tir da HKI kan hare-haren da take ci gaba da aikatawa a Yemen, din da Siriya da kuma Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted