Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Tarihi Ba Zai Yafe Jinkirin Yin Allah Wadai Da Bala’in Gaza Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai yafe jinkirin yin Allah wadai da bala’in Gaza ba Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarihi ba zai yafe jinkirin yin Allah wadai da bala’in Gaza ba

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: “Al’umma ta tuna cewa bala’in Gaza bai shafi musulmi kadai ba, wannan lamari ne na gwaji na lamiri na dukkanin bil’adama, don haka suna kira ga dukkanin al’umma ba tare da la’akari da addini ko yanayin kasa ba, da su tsaya a bangaren bil’adama, adalci da mutunci, wato a bangaren dama na tarihi.”

Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araqchi ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a wajen taron baje kolin na majalisar ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, inda ya yi jawabi ga takwarorinsa na kasashen musulmi.

Ministan harkokin wajen kasar ya jaddada cewa yunwa da tashin bama-bamai sun zama laifuffukan yaki da cin zarafin bil’adama, kuma abin da ke faruwa a gaban idanun duniya shi ne yadda wata gungun mutane mai nuna wariyar al’umma da ke gudanar da ayyukanta ba tare da wani hukunci ba.

Araqchi ya ba da shawarwarin daukar matakin da kasashen musulmi za su yi domin dakile wadannan kisan kiyashi da laifukan da ake yi kan al’ummar Falastinu. Ya ce, “Dole ne a dauki kudurin aniyar yin amfani da dukkan hanyoyin da za a bi wajen yin matsin lamba daga kasa da kasa kan ‘yan wariyar al’umma, da hukunta duk wadanda suka aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a Falasdinu, da kuma fuskantar hadin kan kasashen da ke bai wa ‘yan mamaya makamai da kuma kare ta daga tofin Allah tsine.” Ya bayyana cewa Gaza ta wuce wurin jin zafi kawai, kuma mutanen Gaza suna jiran taimakon al’umma na zahiri. Dagewarsu tana kiran al’ummu da mu tsaya tare da su, ba kawai da magana ba, amma da ƙwaƙƙwaran matakai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted