Makami Mai Linzamin Sojojin Yemen Ya Zame Mafarki Mai Firgitarwa Ga ‘Yan Sahayoniyya

Makami mai linzami na Yemen na fission ballistic shi ne babban mafarkin da ke firgita ‘yan sahayoniyya Jaridar Isra’ila, The Jerusalem Post, ta yi bayanin

Makami mai linzami na Yemen na fission ballistic shi ne babban mafarkin da ke firgita ‘yan sahayoniyya

Jaridar Isra’ila, The Jerusalem Post, ta yi bayanin cewa: Harba makamai masu linzami na gungu fission ballistic daga Yemen yana kara yawan barazanar tsaro, tare da dagula Shirin kakkabo shi, kuma yana janyo wahalar murmurewa daga barnarsa.

Jaridar ta ce amfani da makamai masu linzami na gungu fission ballistic da ‘yan Yemen suka yi a kan abokan gabar Isra’ila na wakiltar wani gagarumin ci gaba mai kunshe da damuwa, tare da lura da cewa wadannan makamai masu linzami suna mayar da tsarin kariya na makamai masu linzami na gargajiya irin su Arrow ko Sling na David marasa amfani saboda ba su da kayan aikin tunkararsa da za su iya dakile bama-bamai da makamin ke watsawa.

Jaridar ta yi nuni da cewa, gazawar tsaron sararin samaniyar Isra’ila wajen hana katsen makami mai linzamin na Yemen ya haifar da tambayoyi masu mahimmanci game da gazawar tsarin tsaron sararin samaniya mai nau’i-nau’i.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted