Shugaban Kasar Faransa Ya Ce: Kakaba Yunwa Laifi Ne Da Ya Wajaba Dakatar Da Ita Cikin Hanzari

Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Kakaba yunwa ga dukkan al’umma laifi ne da ya wajaba a dakatar da ita nan take Shugaban kasar Faransa

Shugaban kasar Faransa ya bayyana cewa: Kakaba yunwa ga dukkan al’umma laifi ne da ya wajaba a dakatar da ita nan take

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce yunwar da al’ummar zirin Gaza suke ciki wani laifi ne da ya zama dole a dakatar da ita nan take.

A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Macron ya kara da cewa a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jiya litinin ya tattauna da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani game da mummunan halin da ake ciki a Gaza.

Ya ci gaba da cewa, “Suna aiki kafada da kafada da Qatar don tabbatar da nasarar kokarin masu shiga tsakani da kuma shirya taron kan abin da ya kira “matsalar kasashe biyu” da za a yi a birnin New York a ranar 22 ga watan Satumba.

Tun daga ranar 2 ga Maris, mamayar ta rufe mashigar Zirin Gaza zuwa shigar da abinci, kayan agaji, agajin jinya, kayayyaki, da man fetur, lamarin da ya haifar da tabarbarewar yanayin jin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted