Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sake nanata kiran da ya yi na a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza a daidai lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kaddamar da wani sabon farmaki na mamaye birnin Gaza da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu.
“Yana da matukar muhimmanci a kai ga tsagaita bude wuta a Gaza nan take, da kuma sakin dukkan wadanda ake tsare da su ba tare da wani sharadi ba, da kuma gujewa kisan gilla da barna da harin soji kan Gaza zai haifar ba makawa,” inji a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin X.
Ya kuma bukaci da a sauya shirin da Isra’ila ta yi na fadada gine-ginen matsugunan da ba bisa ka’ida ba, wanda zai raba yankin yammacin kogin Jordan. Ya kara da cewa, “Duk wani shiri na gina matsugunan ya saba wa dokokin kasa da kasa.”
Isra’ila ta zafafa kai hare-hare kan birnin Gaza a wani bangare na shirinta na kwace yankin tare da mamaye shi baki daya, inda ta tilastawa mazauna birnin Gaza kusan miliyan daya kauracewa gidajensu da kuma rushe gidajen Falasdinawa.
Hamas ta ce Firaministan Isra’ila Netanyahu ya yi biris da yunkurin shiga tsakani na kasa da kasa na tsagaita bude wuta, sannan kuma ya mayar da hankalinsa kawa ikan shirinsa na mamaye birnin Gaza.