Araqchi  Ya Gode Wa Gwamnatin Iraki Da Al’ummarta Kan Kyakkyawar Tarbar Masu Ziyarar Arba’een

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga  Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s}

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Suna godiya ga  Iraki saboda karimcin da ta yi wa masu ziyarar Arba’een na Imam Husain {a.s}

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yaba da kokarin gwamnati da al’ummar Iraki wajen karbar bakwancin masu ziyarar juyayin Arba’een na Imam Husaini {a.s}.

A yayin da yake halartar shirin na musamman na “muryar ku a ko’ina” da ake watsawa a gidan rediyon Saba, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna batutuwan da suka shafi gagarumin tattakin Arbaeen da tasirinsa ga duniyar musulmi.

A farkon hirar, minista Araqchi ya mika sakon gaisuwarsa ga masu ziyarar Arba’een a birnin Karbala, inda ya bayyana farin cikinsa da halartar wannan gagarumin taron juyayi. Yana mai jaddada cewa: “Wannan tattakin babbar yunkuri ne na ‘yan Shi’a, kuma tasirinsa na kasa da kasa yana da matukar muhimmanci, babu wani taro mai girman wannan a duk fadin duniya a duk tsawon shekara.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted