Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi

Rundunar sojan Mali ta sanar da kame wasu manyan hafsoshin sojin Mali guda biyu, dan kasar Faransa, da wasu mutane da dama da ake zargi da yunkurin tayar da zaune tsaye a kasar ta hanyar yunkurin juyin mulki, wanda kuma aka yi nasarar dakile shi.

Ministan tsaron kasar Janar Daouda Aly Mohammedine ne ya bayyana hakan ta gidan talabijin na kasar a yammacin jiya Alhamis, inda ya ce an shawo kan lamarin gaba daya, kuma an fara gudanar da bincike.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tashe-tashen hankula na siyasa, kuma ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ‘yan kwanakin nan kan tsare jami’an soji. Hukumomi sun bayyana dan kasar Faransa Yann Vezilier, inda suka zarge shi da yin aiki “a madadin hukumar leken asiri ta Faransa,” tare da hadin gwiwar shugabannin siyasa, jiga-jigan kungiyoyin farar hula, da kuma sojoji a Mali.

Gidan talabijin na kasar ya watsa hotunan mutane 11 da ake zargin suna da hannu a yunkurin juyin mulkin, wanda hukumomi suka ce an fara shi ne a ranar 1 ga watan Agusta. Kungiyar ta hada da Janar Abass Dembélé, tsohon gwamnan yankin Mopti ta tsakiya, wanda aka kora a watan Mayu bayan ya bukaci a gudanar da bincike kan kisan fararen hula da sojojin Mali suka yi a Diafarabé. Haka kuma an tsare Janar Néma Sagara, wadda ta shahara da rawar da ta taka wajen yakar ‘yan bindiga a shekarar 2012.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted