Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila

Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron A wata gagarumar nuna

Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron

A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” zai fara gabatar da jawabinsa mai kunshe da bayanai neman tunzura jama’a, wanda kuma bayanai suka haifar da cece-kuce a tsakanin wadanda suka zauna suka saurara.

A cikin jawabin shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” ya bayyana cewa; Akwai yiwuwar samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu a wajen yankunan Falasdinu, musamman a biranen London da Paris na kasashen Birtaniya da Faransa.

Wannan matakin na nuna rashin amincewa da yadda yahudawan sahayoniyya suke adawa tare da yin watsi da hakikanin samuwar Falasdinawa da kuma kokarin tauyaye hakkin al’ummar Falasdinu.

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ne ya jagoranci tawagar ‘yan majalisun dokokin kasar Iran zuwa wajen taron da ya hada shugabannin majalisun dokokin duniya karo na shida a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted