Musulmi A Amurka Sun Fara Daukar Matakan Tsaro A Masallatai Saboda Makiya

Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya

Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu.

Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu.

Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar.

Edword yace abu mafi muni da ya faru a cikin kimani shekaru biyu da suka gabata, shi ne ind wani, mutum ya bindige wani yaro dan shekara 6 a duniya, bafalasdine musulmi ya kuma jiwa mahaifiyar yaron rauni.

Yace wadannan shekaru biyu sun yiwa musulmi a Amurka wahala. Musamman idan sun hadu da maso goyon bayan yahudawa a kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted