Miliyoyin Al’ummar Yemen Sun Fito Taron Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Falasdinawa

 Al’ummar kasar Yemen suna ci gaba da nuna goyon bayansu ga Gaza, miliyoyin mutane suka jaddada kiran zafafa kai hare-haren daukan fansa kan ‘yan sahayoniyya

 Al’ummar kasar Yemen suna ci gaba da nuna goyon bayansu ga Gaza, miliyoyin mutane suka jaddada kiran zafafa kai hare-haren daukan fansa kan ‘yan sahayoniyya

Dubun dubatan jama’ar kasar Yemen ne suka fito kan tituna a jiya Juma’a a dandalin Al-Sab’en da ke tsakiyar fadar mulkin kasar Sanaa, da kuma dandali da dama a duk fadin sauran jahohin kasar, domin nuna goyon bayansu ga gwagwarmayar al’ummar Gaza, kuma a matsayin wa’adi na shugabancin kasar Yemen, wanda ya sha alwashin daukar wasu zabukan kara kaimi wajen nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu.

Yemen ta ga wata rana ta musamman tare da jama’a da ba a taba ganin irinsu ba, suna amsa kiran Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi tare da nuna girman bala’in da ke faruwa a Gaza, da suka hada da kisa, kakaba yunwa, da kuma killacewa. Yamanawa sun amsa kiran tare da taron jama’arsu, da rera wakoki, da cikakkiyar shirinsu na sadaukarwa  ga duk wani zaɓi na haɓaka ayyukan soji.

Ministan yada labaran kasar Yemen Hashem Sharaf al-Din ya ce, “Gaza ta yi kira, sannan Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya yi kira, kuma al’ummar Yemen sun mayar da martani ta hanyar zanga-zangar da ba a taba ganin irinta ba. Suna da yakinin cewa wannan gagarumar zanga-zangar za ta haifar da karuwar ayyukan soji da karin zabin da Sayyed Abdulmalik al-Houthi ya yi magana akai, don haka wajibi ne makiya su yi la’akari da wannan gagarumin zanga-zangar.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted