Kungiyar Hamas Ta Yi Fatali Da Mahangar Yahudawan Sahayoniyya Ta Neman Falasdinawa Su Rusuna Musu

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda

Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki.

Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a yi a sake su sai ta hanyar sharuddan da ‘yan gwagwarmaya suka gindaya.

Ya jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu gindaya sharudda, kamar yadda ta sanya ma’aunin da ya dace abi.

Kafofin yada labarai sun ambato Netanyahu yana fadar haka daga Washington cewa: Dole ne Gaza ta samu wata makoma ta daban, kuma har yanzu dole ne su kammala aikin sakin dukkan fursunoni tare da kawar da karfin soji da na gwamnatin Hamas gaba daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted