Amurka Tana Fatan HKI da Hamas Su Tsaida Budewa Juna Wuta Na Kwanaki 60 A Karshen Wannan makon

Jakadan Amurka na musamman a yankin yammacin Asiya Steven Witkoff ya bayyana cewa yana fatan HKI da kuma kungiyar Hamas zasu cimma yarjeniyar tsagaita budewa

Jakadan Amurka na musamman a yankin yammacin Asiya Steven Witkoff  ya bayyana cewa yana fatan HKI da kuma kungiyar Hamas zasu cimma yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta a karshen wannan makon.

Jakadan ya kara da cewa idan har yarjeniyar ta tabbata, kungiyar Hamas zata mikawa HKI yahudawa masu rai 10 da kuma gawakinn wasu 09 .

Steven Witkoff bai bayyana abinta ita Hamas da kuma sauran Falasdinawa zasu samu a wannan yarjeniyar na kwanaki 60 ba. Musamman bayan ta rasha falasdinawa kimani 57500 ya cikin watanni kimani 21 yahudawan suna fafatawa da ita ba.

Har’ila yau falasdinawa 150,000 suka ji rauni mafi yawansu mara da yara. A cikin wadanda aka kashe akwai yara kimani 12, 000

Daga karshe Witkoff, yace a halin yanzu sabani guda ne kacal ya rage ba’a warware ba, cikin guda hudu da ake tattaunawa da Hamas na lokaci mai tsawo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted