HKI Ta Kashe Falasdianwa 6 A Gaza, Kuma Tsoffin Fursinoni

Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da

Wani babban jami’I a kungiyar Hamas ya bayyana cewa sojojin HKI sun kashe falasdinawa guda 6 a zirin gaza a ci gaba kissan kiyashin da takewa falasdinawa a yankin.

Abdul-Karim Hanini, ya kara da cewa wadanda ta kashen tsoffin fursinoni a hannun yahudawan a shekarun da suka gaba 5 daga cikinsu an yi musayarsu ne a shekara 2011 a lokacinda aka yi musayarsu da fursinan yahudawan Galid Shalit a shekarar. Sannan dayan kuma an yi musayarsa ne a shekara ta 2002 wanda yahudawan suka kora daga Cocin Nativity daga birnin Bethlaham a yankin yamma da kogin Jordan.

Abdul-Karim Hanini  ya kammala da cewa a dai dai lokacinda muke makokin yan’uwammu da yahudawan suka kai ga shahata, muna rokon All..ya karbi shahadarsu, sannan muna kara nanata cewa zamu ci gaba da gwagwarmaya da su har zuwa jinni na karshe da zamu iya zubarwa ko kuma mu sami nasara a kansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted