Wani Fim Din Iran Ya Sami Kyauta A Baje-Kolin Fina-finai Na Shanghai

Fim din  Iran mai taken: Akharin Kuse Nahang” wanda Ramtin Balf ya shirya shi ya samu kyauta a baje kolin fina-finan ta Shangahi. Shugaban ma’aikakar

Fim din  Iran mai taken: Akharin Kuse Nahang” wanda Ramtin Balf ya shirya shi ya samu kyauta a baje kolin fina-finan ta Shangahi.

Shugaban ma’aikakar al’adu da koyarwar musulunci ta Iran a yankin Bu-Shehr Muhammad Hussain Zaduyan ya sanar da cewa; Fim din wanda na ilmantarwa ne, yana daga cikin fina-finai masu muhimmanci da aka fitar da shi a Iran.

Shi dai wannan bikin  na baje kolin fina-finai a Shanghai an yi shi ne daga ranar 3 ga watan Yuli zuwa 7 ga gare shi a wannan shekarar ta 2025.

An yi wannan bikin ne na baje-koli ne a daidai lokacin da ake yin taron kungiyar “BRICS” da taron kasashen Asiya.

Zanduyani ya kuma ce; Fim din na Iran wanda yake Magana akan matsalar da ake fuskanta ta karewar wasu daga cikin halittun ruwa, kamar kifin “Shakes” ya sami kyautar a wurin wannan taron na baje koli wanda shi ne karo na 17.”

Karamin ofishin jakadancin Iran a kasar China wanda yake kula da yada ala’adun Iran, shi ne ya wakilci wanda ya shirya fim din wajen karbar kyautar da aka ba shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted