Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila

Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai

Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu..

Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.  

Yana mai jaddadad cewa: Yakin da ‘yan gwagwarmaya ke yi da makiya daga arewacin Zirin Gaza zuwa kudancinta, zai kara haifar da hasara ga ‘yan mamaya a kowace rana, kuma ko da kuwa a ‘yan kwanakin nan sun samu nasarar kubutar da dakarunsu gwagwarmaya daga wani makircin ‘yan mamaya tare da killace sojojin mamayar Isra’ila da haka ya Sanya suka kara kama fursunonin yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted