Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta a nan Iran ta fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa a ziyarar da Benyamin Natanyaho yake yi a halin yanzu a kasar Amurka ya nuna cewa yana son ci gaba da yaki da kasar Iran sannan da alamun shugaba Trump yana tare da shi.
Labarin ya kara da cewa matsayin shuwagabannin biyu a yanzun bai da bambanci bayan yakin kwanaki 12.
Majiyar ta bayyana cewa Iran a shirye take ta kare kanst, kuma tana ganin ziyarar da Natenyahu yake yi a Amurka duk yaudara ce, saboda tuni sun rika sun yanke shawara kan ci gaba da yaki.
Dangane da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kuma, majiyar ta ce, Idan Trump yana ganin da sauki za mu sake komawa kan teburin tattauna da shi, yana rudar kansa ne.