Janar Ali Fadli: IRGC Suna Da Damar Kera Makamin Nukiliya Da Kuma Rufe Mashigar Ruwan Hurmuz

Janar Ali Fadi wanda tashar talabijin din Iran ta yi hira da shi a jiya da dare, ya bayyana cewa; Iran tana da damar kera

Janar Ali Fadi wanda tashar talabijin din Iran ta yi hira da shi a jiya da dare, ya bayyana cewa; Iran tana da damar kera makamin Nukiliya da kuma rufe mashigar ruwan Hurzum.

Janar Fadli ya ce; Dakarun na kare juyin musulunci sun lakanci yadda ake kera shi, tare da bayyana fatan cewa kar  makiya su tafka  babban kuskuren da zai tura Iran yin tunanin hakan.”

Dangane da batun rufe mashigar ruwan Humuz kuwa, janar Faldi ya ce, suna da damar yin hakan,sai dai kuma ko kadan wannan ba ya cikin manufofin jamhuriyar musulunci.

Janar Fadli shi ne mai kula da tafiyar da ayyyuka a tsakanin bangarori daban-daban na dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted