Jalali: Mun  Hana Fitowar Sanadarorin Nukiliya Ta Hanyar Aiki Da Ka’idojin Tsaro

Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za

Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za su iya cuta da mutane.

 Kamfanin dillancin labaru na “Mehr” ya nakalto janar Jalali yana cewa; Amurka ta kai hare-hare akan muhimman cibiyoyinmu da suke dauka cewa yana da girma da tsanani, sai dai mun dauki matakai na kariya da su ka hana fitowar sanadarori na Nukiliya da za su iya zama masu hatsari da cutarwa ga mutane.

Janar Jalali ya ce, tun a lokaci mai tsawo ne aka dauki wadannan matakan saboda kaucewa bacin rana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted