Malaman Sunna A Kasar Iran Sun Bayyana Gwagwarmaya Da HKI Wajibi Ne A Sharia

Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia.

Malaman addinin musulunci daga mazahabar sunna kima 1300 sun tabbatar da cewa gwagwarmaya da HKI wajibi ne a addinin musulunci kuma wajibi ne a Sharia.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin da malaman suka fitar bayan taron da suka gudanar na cewa tallafawa falasdinawa wadanda HKI take kashewa wajibi ne a sharia. Kuma suna kira ga dukkan malaman sunnan su gane haka su kuma bayyanawa sauran musulmi musamman ahlussa kan cewa jihadi a kan yahudawa sahyoniyya wadanda suke mamaye da kasar Falasdinu wajibi ne ga wanda yake da ikon  hakan.

Bayanin ya kara da cewa abinda Falasdinwa suka yi a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023M da kuma fara yakin Tufanul Aksa yana dai dai da sharia.

Daga karshe bayanin ya kara da cewa HKI ta kusan Rushewa. Sannan mamayar da kasashen yamma sukewa kasashen musulmi ya kusan kaiwa ga karshe idan All..ya yarda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted