Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu.
Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.”
Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da matsoratan ‘yan sahayoniyya suka yi wa kisan gilla, dukkansu suna dauke da sako karara.
Araqchi ya ci gaba da cewa: Sabanin gwamnatin ‘yan sahayoniyya masu Rauni, marasa karfi, Iraniyawa ba su taba boye hasarar da aka yi musu. Suna alfahari da shahidansu, su ne abin koyinsu. Ku tabbatar cewa, kowane jami’i ko masanin kimiyya da Iran ta rasa, akwai É—aruruwan da suke layi don maye gurbinsu.
Ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu karfi da juriya za su tsaya tsayin daka har sai digon jini na karshe a kan duk wanda ke son yanke hukunci kan makomarsu.